Ofishin jakadancin Amurka yace an janye gargadin ne ganin yadda aka karfafa daukan matakan tsaro a zagaye da duk sassan yankin da Otel din Hilton, da Nicon da kuma Sheraton suke, kazalika an karfafa matakan tsaro a kewayen dukkan gine-ginen Gwamnati da muhimman hanyoyin shiga da fita daga Abuja.
A wani labarin kuma, kungiyar kare hakkin Bil Adama ta kasa da kasa (Amnesty) a yau Alhamis tayi kira ga kamfanin man fetur na Shell da ya kokarta samar da kudi Dala miliyan dubu domin a fara aikin tsaftace yankin da rijiyoyin man na biyu suke a yankin kudu maso gabashin Nigeria. Kungiyar tace lafiyar al’ummar dake zaune a yankin na fuskantar barazana musamman ma manoma da masu kamun kifi. Kungiyar Amnesty tana mai cewa lauyoyin dake bada kariya ga al’ummar yankin da matsalar tafi shafa sune wadanda ke zaune a Bodo, Ogoniland yankin Niger Delta inda aka sami hujewar rijiyoyin man dake zuba gurbatacen mai sama da ganga dubu hudu a kowace rana.