Jami’an gwamnatin kasar Afghanistan sun ce wani dan harin kunar bakin wake da motar boma-bomai ya farma wani ayarin motocin sojojin taron dangin kasashen waje a Kabul babban birnin kasar, ya halaka mutanen da yawan su ya kai goma.
Hukumomi sun ce dan kunar bakin waken ya kai harin ne takanas a yau Asabar kan wata mota kirar bas ta kungiyar kawancen tsaron NATO a unguwar Darulaman.
Wani kakakin ma’aikatar ministan cikin gida ya fada cewa a cikin wadanda harin ya rutsa da su akwai fararen hula ukku da jami’in ‘yan sanda daya.
Wata sanarwar da NATO ta gabatar, ta ce rahotannin farko sun nuna cewa an samu dimbin mace-mace a cikin sojojin Afghanistan da na taron dangin kasashen waje.
A cikin wani lamari da ya wakana daban a yau Asabar kuma a kudancin kasar ta Afghanistan, NATO tace sojoji biyu sun mutu lokacin da wani mutum sanye da kayan sojin kasar Afghanistan ya bude wuta kan sojojin Afghanistan da na taron dangin kasashen waje.
Kungiyar kawancen tace an kashe mutumin a lokacin da ya bude wutar.
A halin da ake ciki kuma, hukumomin Afghanistan sun ce a gabashin kasar wata mace ‘yar kunar bakin wake ta ragargaza kan ta da boma-bomai a kofar ma’aikatar leken asirin kasar ta Afghanistan.
Jami’ai sun ce a yau asabar matar ta kai hari takanas kan hukumar leken asirin kasar Afghanistan a lardin Kunar. Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya ce jami’an tsaro biyu sun ji ciwo a cikin harin.