Masu zaman makoki a arewa maso gabashin Najeriya suna shirye shiryen binne dumbin mutanen da aka kashe a hare haren boma bomai da kuma bude wuta da kungiyar Boko Haram tayi kan al’umma.
Jami’an aikin jinkai a Najeriya sun ce a kalla mutane 65 suka mutu a tashe tashen hankali da ake yi a arewa maso gabashin kasar, bayan hare haren da aka kai a garin Damaturu.
Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin hare haren da kuma tagwayen hare haren da aka kai a Maiduguri inda kakakin kungiyar ya yi gargadi da cewa, za a kara kai wadansu hare hare nan gaba. Kakakin shugaba Goodluck Jonathan ya bada sanarwa inda ya bayyana yin Allah wadai da hare-haren bisa ga cewarshi, hare haren sun sa shugaban kasa ya fasa halartar auren kanenshi a jihar Bayelsa dake kudancin kasar.
Kwamitin sulhu na MDD a cikin wata sanarwa ya yi allah wadai da tashe tashen hankalin tare da taya dangin mamatan jajen rashin. Kwamitin sulhun ya kuma yi kira ga jihohin da abin ya shafa su dauki kwararan matakan shawo kan ayyukan ta’addanci bisa la’akari da dokokin kare hakin bil’adama da na ‘yan gudun hijira da kuma ayyukan jinkai.