Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Gargadin Yiwuwar Karin Hare hare a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya


Wani dan sanda ke gadi a wani lungu a birnin Maiduguri
Wani dan sanda ke gadi a wani lungu a birnin Maiduguri

Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya yi gargadi game da yiwuwa

Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya yi gargadi game da yiwuwar wasu karin hare-hare, ‘yan kwanaki bayan da wasu jerin hare-hare a arewacin Nijeriya sun hallaka mutane sama da 100.

Ofishin Jakadancin ya ce ya sami bayanan da ke nuna cewa mai yiwuwa tsattsaurar kungiyar Islamar nan ta Boko Haram ta kai hare hare kan otal-otal da wasu wuraren kuma a babban birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, a lokutan hutun Sallah. Sanarwar, wadda aka sanya ta a dandalin intanet na Ofishin Jakadancin, ta bayyana wuraren da watakila a kai masu harin da cewa sun hada da otal otal da dama da jami’an diflomasiyya da ‘yan siyasa da ‘yan kasashen waje kan sauka.

A watan Agusta da ya gabata, kungiyar Boko Haram ta dau alhakin kai hari kan hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya a Abuja, da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Ana kuma zargin kungiyar kan tashe-tashen hankulan na ranar Jumma’a, a lokacin da ‘yan bindigar su ka auna ofisoshin ‘yan sanda, da Majami’u da kuma sansanonin soji a kananan garuruwa a arewacin Nijeriya. Wannan na daya daga cikin ranaku mafiya muni a tarihin hare-haren kungiyar.

Hare haren sun gamu da Allah wadai daga Kwamitin Tsaron MDD da Paparoma Benedict, wanda a jiya Lahadi ya gaya wa masu ibada cewa tashin hankalin zai haddasa kiyayya da gaba ne kawai.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG