Jami’an Najeriya sun ce a kalla boma bomai uku suka tashi a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar, da kuma wani birni dake makwabtaka da jihar jiya jumma’a.
Shaidu sun ce fashe fashen sun afku ne daya bayan daya a Maiduguri inda gwamnati take dorawa kungiyar kishin Islama mai tsats-tsauran ra’ayi Boko Haram, alhakin karuwa tashe tashen hankali a jihar.
Hukumomi sun ce daya daga cikin fashe-fashen, harin kunar bakin wake ne sai dai, ‘yan kunar bakin waken ne su biyu kawai suka mutu. Bisa ga cewar jami’an tsaro, mutanen sun kai hari ne kan wani sansanin soji inda rundunar tsaron da aka dorawa alhakin kare al’ummar jihar daga hare haren kungiyar suke zama, sai dai basu iya shiga sansanin ba, saboda haka suka tarwatsa nakiyarsu a kofar shiga.
Jami’ai sun ce wata fashewa kuma ta faru wata makarantar Islamiya inda mutane suka taru domin sallar jumma’a. Sai dai babu tabbacin jin rauni ko asarar rayuka.
Yan sanda har wa yau sun bayyana tashin wani bom a wani caji ofis dake jihar Yobe.
Ranar alhamis rundunar ‘yan sanda ta ce dakaru a Maiduguri sun fara bincike gida gida da nufin gano makamai da kungiyar Boko Haram ke iya amfani su.