Yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai Alhaji Bamanga Tukur shugaban tsohuwar PDP ya ce zasu ladafta duk wadanda suka yi tawaye bisa ga dokokin jam'iyyar da na kasa. Ya ce babu wani bangaren jam'iyyarsa da ya balle. Kuma shi yana nan rike da ita daram. Ya ce zasu bukaci jami'an tsaro su yi diran mikiya kan duk wadanda suka ware daga garesu. Bamanga Tukur ya kara da cewa zasu sanar cewa sun ma sauka daga kujerunsu.
Sanato Abubakar Gada mai taimakon Bamanga Tukur ya ce sun dauki tsatsauran matakin ne domin 'yan tawayen sun karya doka kuma dole ne a ladaftar dasu. Ya ce kowane mukami mutum ke rike dashi ya sameshi ne karkashin jam'iyya, jam'iyya kuma ta fi kowa girma. Don haka duk wanda ya ja da jam'iyyar dole ya kuka da kansa.
Yanzu sai a sa ido a gani domin sabuwar PDP ta shigar da kara tana cewa a soke zaben da jam'iyyar ta yi makon jiya kana a kori Bamanga Tukur domin shi ba dan PDP ba ne. Da alama dai duk wata hanya ta sulhu ta rushe.
Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.