Ganin irin yadda maroka ke cin karensu ba babbaka ya sa kungiyar makafi ta arewa ta yi wani taro a Abuja wanda ya samu hallartar duban makafi. Bayan taron nasu sun yi barazanar mamaye birnin idan aka cigaba da hana su yin bara a birnin domin gwamnati bata cika alkawarin da ta dauka ba cewa zata basu jari su yi kasuwanci domin su daina barace-barace. Sun ce muddin ba'a daina kutunta masu ba zasu tare a Abuja idan hukuma ta ga dama ta hallaksu duka.
Muktari Sale kakakin makafin arewa ya kara yin bayani. Ya ce sun ba gwamnatin tarayya wa'adi daga yanzu har zuwa ashirin da tara ga watan Oktoba idan ba'a daina kama mutanensu ba to zasu fito su yi zaman dirshan a Abuja. Ko gwamnati ta biya masu bukata ko kuma ta kaisu wata kasa idan su ba 'yan Najeriya ba ne ko kuma ta sa fetur ta kone su tun da su ba mutane ba ne kuma gwamnatin bata son nakasassu.
A wata sabuwa kuma dan kwamitin zartaswa ta jam'iyyar PDP Tafida Masinja ya umarci shugabannin sabuwar PDP da bangaren Bamanga Tukur da su nemi sasantawa domin ya hango abun da ka faru nan gaba idan ba'a yi sulhu ba.
Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.