Yayin da kwamitin ya isa Jalingo an kusa a kwashi 'yan kallo a gidan gwamnatin Taraba domin jami'an tsaro dake gadin gidan sun hana 'yan jarida da suka biyo kwamitin da aka turo ganin gwamna Danbaba Suntai. Manufar zuwan kwamitin shi ne ya warware dambarwar siyasar jihar da aka shiga tun dawowar gwamna Suntai daga jinya. Jami'an tsaro sun dage babu ganinsa balantana tautaunawa da shi ko daukan hotuna.
Tun farko shugaban kwamitin Sanato Ozodimma ya ce sun zo su ga gwamnan da bangarorin da abun ya shafa. Bayan sun yi hakan kana su yi bayani. Ya ce mun zo ne mu gana da 'ya'yan jam'iyyar PDP da gwamnan domin a kawo karshen cece-kuce. Ya ce can baya sun ziyarci gwamnan a Amurka.
Daya daga cikin dattawan PDP a jihar Buba Yarma Mapindi ya ce yanzu da kwamitin ya zo zasu nemi daidaitawa da junasu. Ya ce akwai batun kundin tsarin mulki ciki kuma majalisar dokokin jihar ta dauki matakin da ya dace. Ya ce idan ka ga gwamna Suntai zaka san ba zai iya aikinshi ba.
To sai dai wadanda suke so gwamna Danbaba Suntai ya cigaba da aikinsa kamar Emmanuel Boacha wanda ya ce ba dole ba ne gwamnan ya fito ya yi jawabi ya kamata a bar gwamnan ya koma kan kujerarsa. Yin jawabi ga mutane ganin dama ne.
Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani