Rahotanni dake fitowa sun ce shugaba Jonathan ya gana da gwamnonin da suka yiwa jam'iyyar tawaye suka kafa abun da suka kira Sabuwar PDP. Bisa ga duk alamu wannan wata muguwar guguwa ce dake neman wargaza jam'iyyar. Tambaya nan itace ana iya shawo kan lamarin cikin dan lokaci karami? Ta bakin Sanato Saidu Kumo yace abun da gwamnonin suka yi tawaye ne. Bai kamata su yi shi a wajen taro da duk duniya ke gani ba. Ya ce akwai gwamnan da zai yadda wani shugaban karamar hukuma a jiharsa ya fita daga inda yake taro dasu ya kwana lafiya? Ya ce kamata ya yi da basu zo taron ba gaba daya. Ya kara da cewa 'yan kudancin Najeriya suna ganin reni arewa ta yiwa shugaba Jonathan domin da a ce shugaban dan arewa ne ba zasu yi masa haka ba. Tamkar an fara dauko wata hanya ta raba kasa ke nan.
Wasu matasa gani suke ba dabara ba ce kafa jam'iyya cikin jam'iyya. Bunu Yadi ya ce kana cikin PDP ka ce ka kafa wata PDP kana zolayar kanka ne kawai. Idan zasu fita su fita su kafa wata jam'iyya tasu daban. Ya ce kawunan matsa sun waye. Wadannan da suka fita karya suke yi. Suna zolayar mutane ne kawai. Ya ce su suna tare da gwamnatin Jonathan dari bisa dari. Basa tare da makaryata.
Sai dai sakataren ma'aikatan gidan gwamnatin Adamawa Abba Jimeta ya ce zasu kai PDP karkashin shugabancin Bamanga Tukur gaban kotu domin ta ci mutuncin Alhaji Atiku Abubakar a babban taronta na ranar Asabar da ta gabata. Ya ce inda da mutunci bai kamata a ce Atiku na runfar Adamawa ba. A matsayinsa na rike mukamin mataimakin shugaban kasa har shekaru takwas kamata ya yi a ce yana tare da manyan shugaban jam'iyyar.
Wata majiya kuma ta ce sabuwar PDP din karkashin Kawu Baraje zata kafa ofisoshi a duk fadin kasar sai dai jami'an kasar su yi masu dirar mikiya. Idan ko hakan ya faru kila sai dai koyu ta yi hukunci.
Ladan Ibrahim Ayawa nada karin bayani.