Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mafi Cancanta Ne Zai Zama Dan Takarar Shugaba a APC


Jigon APC Alhaji Attahiru Bafarwa
Jigon APC Alhaji Attahiru Bafarwa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce jam'iyyar APC za ta zabi mutum mafi karbuwa a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce sabuwar jam'iyyar su ta APC za ta tankade ta rairaye wajen zaben dan takarar Shugaban kasa ta yadda sai wanda jama'a ke so ne zai zama shugaban kasa.

A wata hirar da ya yi da Sashin Hausa a yayin da ya kawo wata ziyara a nan birnin Washington, Bafarawa ya ce jam'iyyar ta APC za ta kuma yi komai a bayyane tare da mutunta dukkannin ka'idojin jam'iyyar.

Ya ce jam'iyyar ba za ta wargaje kokacin zaben dan takara Shugaban Kasa ba. Bafarawa, wanda bai bayyana matsayinsa kan takara ko rashin takarar Janar Muhammadu Buhari ba, ya ce jam'iyyar za ta yi adalci ga dukkan 'yan masu sha'awar zama 'yan takara kuma a karshe jama'a ne za su zabi dan takarar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG