Gwamnonin sun tattauna a kan batun gyaran kundin tsarin mulkin kasa, suka kuma amince da tsarin tarayya, tsarin da ya karfafa Najeriya ta kasance dunkulalliyar kasa, kuma suka ce duk wata kwaskwarima da majalisar tarayya zata yi kan mulkin kananan hukumomin zai raunana tsarin tarayya da yanzu ake gudanarwa.
Da yake karanta sanarwar bayan taron ga manema labarai, gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayomi yace, taron gwamnonin na APC ya tattauna batun rarraba arzikin kasa. Yace duk da shawarwari da aka ba shugaban kasa, babu wani yunkurin da aka yi na kara kason da ake ba jihohi da kananan hukumomi, duk da yake nan ne al’ummar kasar suke zaune.
Gwamnonin sun kuma jaddada goyon bayansu ga masu rikon jam’iyar a matsayin kasa, domin ganin an yi tafiya tare da duk wanda ya shiga jam’iyar ta APC.
Mai masaukin baki gwamnan jihar Nassarawa ya yaba goyon bayan da jama’a suka bayar na ganin an yiwa jam’iyar rajista ya kuma bada tabbacin cewa, jam’iyar ba zata basu kunya ba.
Ga Rahoton da Wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji.