Duk da darewar jam'iyyar gida biyu jam'iyyar ta gudanar da zaben shugabanninta na kasa. Cikin wadanda aka zaba har da Barrister Ibrahim Abdullahi Jalo a matsayin mataimakin kakakin jam'iyyar na kasa wanda ya ce PDP daya ce babu wata PDP kuma.Ya ce ba'a fada masu cewa akwai baraka a jam'iyyar ba kuma babu wanda ya fito ya ce shi baya cikin PDP. Idan wani ya fito ya ce shi yana cikin sabuwar jam'iyyar PDP to abun da Bamanga Tukur ya ce zai yi ke nan. Duk wanda ya yi fushi idan ba wata jami'iyya ya koma ba to yana karkashin Bamanga Tukur.
Barrister Jalo ya yadda cewa an san akwai jayayya tsakanin wasu gwamnoni da uwar jam'iyya kuma ana kokarin sasantawa domin shugaban kasa da tsohon shugaban kasa Obasanjo suna tattaunawa dasu. Ya ce babu shakka gwamna Kwankwaso ya shigo taron daga baya ya bace. Haka ma gwamnan Adamawa wanda ma har sai da ya gaisa da shugaban kasa.
Dangane da abun da sabbin shugabannin zasu yi su kawo masalaha Barrister Jalo ya ce babu abun da zai kawo daidaitawa sai an zauna an tattauna. Ya ce alamar cewa za'a warware rikicin shi ne su 'yan tawayen basu fita daga jam'iyyar ba. Hakan ya nuna suna neman gyara ne.
Ga rahoto.