Tun kafuwar jam'iyyar PDP ba'a taba samun wani lokaci da hekwata din ta zama wara-wara kamar 'yan kwanakin nan ba domin yawancin taronta ana yi ne a gidajen wasu ko kuma a fadar shugaban kasa. Matasan sabuwar PDP sun yi gangami a bude masu hekwatar sabuwar jam'iyyar amma tun da yake gwamnonin aware da suka shugabanci darewar PDP sun koma jihohinsu sai suka jirkinta.
Alamu na nunawa cewa idan sabuwar PDP bata yi kaye ba to ana iya yin angulu da kan zabo ko kuma a raya jam'iyyar PDM wadda Alhaji Abubakar Atiku ya ce ba sabuwar jam'iyya ba ce. Ya ce PDM kungiya ce da ta na nan tun lokacin Babangida wanda ya ki ya yi mata ragista. Haka ma Abacha bai yi mata ragista ba. Amma a lokacin Abdulsalami ta hade da PDP. Ita ce kungiyar da ta fi karfi a cikin PDP. Bayan an kafa PDP wasu sun shiga ANPP, wasu kuma sun shiga AD amma duk da haka suna tafiya tare a kungiyance.
Wani abu da ya nuna cewa lamarin ya yi zafi shi ne rashin martani mai zafi daga Bamanga Tukur da shugaba Jonathan da yanzu suke neman a yi sulhu ta hanyar amintattu kamar Tony Anenih. Yanzu hankula sun koma kan ko wanene ke rike da takardar ragistar PDP
Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.