Dangantaka tsakanin Goodluck Jonathan da Wammako tayi tsami ne saboda badakalar zaben gwamnan jihar Ribas, Rotimi Ameachi a matsayin shugaban dandalin gwamnonin Najeriya.
Ibrahim Adamu Tudun Doki dan majalisar matasa ta kasa ne, yace dalilin cire wannan minister na da alaqa da siyasar Shugaban Najeriya da Gwamnan jihar Sokoto. Gwamnan Sokoto dai baya goyon Goodluck ya cigaba da mulki. Akwai adawa tsakaninsu da gwamnan, kuma tsige shi zai saka shugaban ya kawo wanda yake so kan karagar mulki, sannan ya raba hankulan mutanen Sokoto ‘yan jam’iyyar PDP, sannan zai samu goyon baya idan zaben shugaban kasa yazo, kuma ya kara wa gwamnan jihar Adawa, amma ba don koke-koken matasa ba, ko dan yana so ya kyautata wa matasan Najeriya.
Masana kimiyyar siyasa a Najeriya na ganin wannnan lamari a matsayin koma baya ga demokradiyyar Najeriya.
Dr. Yahaya Tanko Baba shine shugaban sashen nazarin siyasa a jami’ar dan fodio a can Sokoto.
“Wannan yana nuna irin tabarbarewa na harkokin mulki da gudanar da al-amuran mutane a Najeriya yake ciki. Mutane sun kasa fahimtar dalilin cire shi, saboda babu wani dalili da aka bayar. Amma kai tsaye mutane suna iya yin la’akari cewa, dalilin kuwa bashi da nasaba da irin takon sakar da ake tsakanin gwamnan jihar Sokoto, da gwamnatin tarayya, ko da jam’iyyar PDP ita kanta.