Wasu mahara sun kashe mutane 15 a kauyukan Abonong da Zayit dake karamar hukumar Barikin Ladi, ta jihar Filato, ciki har da wani limanin coci da matarsa da ‘ya ‘yansa uku.
Rundunar tsaron sojoji na mussaman a jihar Pilato ta ce ta saka matakan tsaro a kan titunan jihar gaba daya don tabbatar da cewa anyi bukukuwan babbar Sallah lami lafiya.
Ganin yadda matsalolin tsaro suka addabi wasu sassan jihar Filato ya sa gwamnatin kasar Jamus ta yunkuro don taimakawa ta hanyar horas da shugabannin kungiyoyin al’umma.
Wadansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi kwantan bauna suka kashe matafiya biyu a kauyen Kassa dake karamar hukumar Barkin ladi ta jahar Pilato.
Rundunar tsaro ta musamman a Jahar Pilato tace ta samadda wassu kayayyakin aiki, kwatankwacin wadanda ake amfani dasu a kasashen da suka ci gaba, wajen gano masu aikata laifi a tsakanin al’umma.
Shugaba Muhammadu Buhari zai karrama Imam Abdullahi Abubakar, wanda da ya bai wa kiristoci fiye 300 mafaka a masallaci da gidansa a lokacin da rikici ya barke a Barikin Ladi na baya-bayannan a Jihar Filato.
Masana sun bukaci hadin kan al'umma da gwamnatoci don kawo karshen zubda jini da aka kwashe fiye da shekaru 20 ana yi a jihar Filato da wasu sassan Najeriya.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Bom dake kan iyakar kananan hukumomin Barikin Ladi da Mangu, kusa da marabar Kantoma inda suka kashe mutane shida.
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce zata zauna da dukkanin jami’an tsaron kasar don bayyana musu matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar da nufin kawo karshensu
Rundunar tsaro ta musamman a jihar Filato ta ta cafke mutane 17 ake zargi da haddasa rikicin jihar da yayi sanadiyar rasa rayuka.
Hukumar wanzar da zaman lafiya da sulhu a Jihar Filato ta yi kira ga daukacin al'umma da su hada kai da masu ruwa da tsaki domin samar da zaman lafiya mai dorewa.
Al’umomin Fulani da na Birom dake karamar humar Barikin Ladi a jihar Filato, sun bukaci hukumomin tsaro da su dukufa wajen gudanar da aikinsu na tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.
Al'ummar Jihar Filato sun bayyana ra'ayinsu game da hukuncin da kotu ta yankewa tsohon Gwamna Jihar Joshua Dariye.
Rundunar 'yan sanda jihar Filato ta bayyana damuwa kan yawaitar fyade da ake wa kananan yara a jihar.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da mutuwar wasu ‘yan Sanda uku dake kwantar da tarzoma a wani kwantan bauna da wasu mahara suka yi musu a mararrabar Udege.
Kungiyar al’ummar Berom dake fadin Jihar Filato ta yi kira ga gwamnatocin tarayya da ta jiha, da su dauki matakan gaggawa wajen dakatar da kashe-kashen da ake yiwa jama’a a wasu sassan jihar.
Hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defense a jihar Nasarawa ta yi nasarar cafke wasu mutane dake tafka manyan laifuka, ciki har da wasu da bindigogi a yankin karamar hukumar Toto da ake rikici.
Babban sakataren kungiyar hadin kan Krista ta Najeriya CAN, Rev Dakta Musa Asake ya rasu ranar Juma’a.
Al’ummomin karamar hukumar Doma jihar Nasarawa sun fara zaman sulhu domin neman mafita daga tashe-tashen hankulan da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya, lamarin da rayuka da dama da dukiyoyi sun salwanta.
A kalla mutum 35 ne aka kashe wasu dayawa kuma suka bace a wani harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Tse Umenger dake karamar hukumar Guma a jihar Benue.
Domin Kari