Da alama umurnin sufeto janar na 'yan sandan Najeriya na kwace makamai daga hannun jama'a ya fara aiki, yayin da Jihar Filato ta ce ta yi nasarar kwace makamai da harsasai da dama.
Al’umomin Fulani da Tiv a jihohin Benue da Nasarawa, sun bukaci gwamnatocin jiha da na tarayya su sake duba yanayin tsaro a jihohin don tabbatar da zaman lafiya.
Gwamnatin jihar Nasarawa tare da hadin gwiwar hukumar tsaro da kare al’umma ta ‘kasa Civil Defense, sun horas da matasa 5,900 kan yadda zasu samo bayanai daga al’umma don hana afkuwar tashin hankali tun kafin ya afku.
Biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin Fulani da wasu al'ummomin jihar Binuwai wanda ya lakume rayuka da dama ya kuma raba wasu da muhallansu, Shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa al'ummar jihar jaje tare da kiran a hada kai a samu zaman lafiya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kai ziyara jihar Benue domin jajintawa da kuma kiran jama’a su a zauna lafiya, saboda rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya da jihar ke fama da su.
Cibiyar warkar da cutar yoyon fitsari ta asibitin Jankwano dake Jos ta yi aiki wa mata 451 cikin wannan shekarar kawai kuma kawo yanzu ta warkar da kimanin mata dubu 10
Gwamnatin jihar Filato ta ce zata bunkasa harkar noma don samarwa da al’ummar Najeriya abinci, a cewar gwamnan jihar Simon Lalong, yayin da yake ganawa da manema labarai da nuna musu taraktoci 400 da gwamnatinsa ta sayo don rarrabawa manoman jihar.
Mutane a Karamar Hukumar Bassa sun wayi gari da tsintar gawarwakin mutane uku da suke zargin junansu da kashewa.
Biyo bayan zanga zangar da matuka kekenapep suka yi a Jos jihar Filato da ya kai ga lalata motocin hukumar FRSC tare da raunata wasu jami'anta, gwamnatin jihar ta dakatar da yin sufuri da kekenapep a Jos da Bukuru matakin da yanzu ya jefa talakawa cikin halin kakanikayi