Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rudunar Tsaron Jihar Pilato Ta Dauki Matakai Yayin Da Sallah Ke Gabatowa


Rundunar tsaron sojoji na mussaman a jihar Pilato ta ce ta saka matakan tsaro a kan titunan jihar gaba daya don tabbatar da cewa anyi bukukuwan babbar Sallah lami lafiya.

Rundunar wanzar da zaman lafiya a jahar Pilato tace ta sanya ingantattun matakan tabbatar da an gudanar da bukukuwan babbar sallah lafiya.

Kakakin rundunar tsaro a jahar pilato Manjo Umar Adam yace rundunar ta jibge jami’anta musamman akan hanyoyi da wurare da tasan akwai matsalolin tsaro.

A halin da ake ciki kuma jama’a na koka tsadar dabbobi da ake yanke yankawa musamman a wannan lokaci na sallar layya.

A cewar Alhaji Shehu Abdulkadir wanda a baya yake yanka sa, bana dai ba tabbas.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG