Kakakin rundunar tsaro ta STF a jihar Pilato, Manjo Umar Adam wanda ya sanar da haka, yace rundunarsu ta dukufa wajen tabbatar da tsaron lafiyar jama’a.
A yunkurinta na shawo kan matsalar tsaro, hukumar tsaron farin kaya ta kasa, ta horadda jami’anta kan amfani da makami da dabarun gano masu aikata laifi, ganin yadda ayyukan ‘yan’fashi da makami da masu garkuwa da jama’a ke kara yawaita a wassu sassan Najeriya.
A hirarsa da Muryar Amurka yayin wani taron karawa juna sani, kwamandan rundunar a jihar Nasarawa, Mohammed Gidado Fari yace bayan horarwa daban daban da suka yi wa jami’ansu manya da kanana, yana da yakinin cewa, tsaro zai inganta a fadin Najeriya.
Yayin wata ziyarar gani da ido da jajinta da ya kawo jihar Plato bayan kashe kashen da suka wakana a wadansu sassan jihar da suka janyo asarar rayuka da dama, mataimakin jakadan Amurka a Najeriya, David Young yace Amurka tana bada gudunmuwa don tabbatar da tsaro a Najeriya ta hanyar horadda jami’an tsaro, shirya taron sasanta tsakanin jama’a, da kuma bada tallafin kudi ga ‘yan gudun hijira.
Mr Young ya bayyana irin kokarin da kasar ke yi wajen samarda tsaro a Najeriya yace “mun tallafa wa kungiyoyi daban-daban dake aikin inganta tsaro da zaman sasantawa, abinda muka tabbatar yana taimakawa, muna kuma horadda Jami‘an ‘yan’sanda a Abuja dake aiki a fannoni daban-daban.”
David Young ya kara da cewa, “a yanzu haka mun samadda fiye da dala miliyan dari biyu don tallafawa ‘yan gudun hijira kimanin miliyan biyar a Arewa maso gabashin Najeriya.”
Saurari Rahoton wakiliyarmu Zainab Babaji
Facebook Forum