Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Filato: ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Karamar Hukumar Barikin Ladi


Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Bom dake kan iyakar kananan hukumomin Barikin Ladi da Mangu, kusa da marabar Kantoma inda suka kashe mutane shida.

Basaraken gargajiya na yankin Barikin Ladi Da Gwom Edward Gyang Bot, ya shaidawa Muryar Amurka cewa a daren jiya Asabar ne maharan suka kai harin, inda aka kashe mutane shida, an kone Majami’a da wani asibiti da kuma wasu gidaje.

An kai wannan hari ne kuwa duk da cewa an zuwa jami’an tsaro a ko ina a yankunan, domin samar da zaman lafiya da hana faruwar ko wanne irin tashin hankali.

Shima sakataren kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar Barikin Ladi, Abubakar Gambo, ya ce suma a jiyan an kashe musu mutane biyar, bayan da mutanen suka fito domin zuwa gaisuwar ta’aziyya nan take sojoji suka bude musu wuta suka kashe su.

Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar sojoji na STF Manjo Umar Adam, amma bai amsa wayar sa ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG