Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Filato: Jami’an Tsaro Sun Cafke Mutane 17


‘Yan sandan Najeriya.
‘Yan sandan Najeriya.

Rundunar tsaro ta musamman a jihar Filato ta ta cafke mutane 17 ake zargi da haddasa rikicin jihar da yayi sanadiyar rasa rayuka.

Kakakin rundunar tsaro ta STF a jihar Filato Manjo Umar Hassan, ya ce uku daga cikin mutanen da aka kama daga yankin Gashish a karamar hukumar Barikin Ladi, an same su da makamai.

Da yake bayyana wadanda aka kama kakakin rundunar ya ce an sami mutanen 13 daga cikinsu da laifin tayar da hankali a cikin garin Jos.

Daga hedikwatar tsaron Najeriya ta tura da wasu sojoji na musamman domin su taimaka wajen samar da zaman lafiya. Haka kuma rundunar sojan sama ta aika da jirage masu saukar ungulu wadanda zasu taimaka wajen yin sintiri ta sararin samaniya.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG