Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Kai Hare-Hare A Pilato


Buhari a Filato
Buhari a Filato

Wadansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi kwantan bauna suka kashe matafiya biyu a kauyen Kassa dake karamar hukumar Barkin ladi ta jahar Pilato.

Sakataren kudi na kungiyar Miyetti Allah a jahar Pilato, Boro Ardo Yakubu, yace mutanen sun fito ne daga kasuwar shanu ta Bukur yayinda maharan suka far musu da misalin karfe takwas na daren jiya lahadi. Ardo Yakubu yace tuni suka shaida wa jamia’an tsaro. Duk kokarin da Muryar Amurka tayi na jin ta bakin jamia’an tsaron yaci tura, domin kuwa wakiliyar Sashen Hausa a jihar Plato Zainab Babaji ta kira lambar kakakin rundunar STF, Manjo Umar Adam sau da dama amma bai dauka ba.

Lamarin ya auku ne kwanaki biyu bayan kisan wadansu mutane uku a kauyen Zanwa dake yankin Miango a karamar hukumar Bassa, wanda daga bisani wadansu matasa suka auka wa wata mota a Rukuba road, suka kona motar da direban a ciki.

A makon jiya ne dai hukumar sasanta tsakanin al’umma a jahar Pilato tayi taron kwana uku da masu ruwa da tsaki don samun daidaituwan lamura bayan kashe-kashen da suka auku a wadansu sassan jahar kwanan baya.

Saurari cikakken rahoton

Ana sake ci gaba da kai hare hare a jihar Plato-3:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG