Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa Na Kalubalantar Takardun Takarar Bazoum Mohammed a Kotu


 Bazoum Mohamed
Bazoum Mohamed

Wasu magoya bayan jam’iyyun adawa a Jamhuriyar Nijar sun shigar da kara a kotun Diffa da nufin kalubalantar dan takarar jam’iyyar PNDS Tarayya Bazoum Mohamed.

‘Yan adawar suna zargin tsohon ministan cikin gidan na Nijar da mallakar jabun takardar shaidar zama dan kasa.

A ranar 11 ga watan Nuwamban 2020 ne wasu ‘yan hamayya da suka hada da ‘ya’yan jam’iyyar MPN Kishin kasa, RDR Canji da kuma Moden Lumana suka shigar da wannan kara a bisa bukatar ganin kotun birnin Diffa ta gudanar da bincike domin tantance sahihancin takardun.

Dan takara a zaben ‘yan majalisar dokokin kasa kuma kusa a jam’iyyar MPN Kishin kasa, Mahaman Tar Choukou, shi ne jagoran wadanda suka kaddamar da wannan yunkuri, ya ce sun gano wasu abubuwa da ba su dace ba a takardun dan takarar PNDS Tarayya shine suka shigar da kara.

Choukou ya kara da cewa suna son kotu ta bincika takardun saboda akwai wasu matsaloli domin ta duba ta ga sun dace da doka ko ba su dace ba.

Da yake maida martani wani na hannun daman dan takarar jam’iyyar ta PNDS, Alhaji Mai Boucar, ya ce basu da fargaba a game da wannan yunkuri na ‘yan adawa, kuma wannan batu akwai siyasa a ciki.

Ya kuma kara da cewa wannan magana ta batun zama cikakken dan kasa ba yau aka fara ta ba, hakama an yi irin wannan akan shugabannin Nijar da aka zaba guda 3 a matsayin shugaban kasa suma ba cikakkun ‘yan kasa ba ne.

A ranar 19 ga watan Nuwamba ne ake saran kotun ta birnin Diffa za ta bayyana matsayinta a game da wannan kara a zaman da za tayi a daidai lokacin da kotun tsarin mulkin kasa anata bangare ke aikin tantance takardun ‘yan takarar da suka cancanci shiga zaben shugaban kasa na ranar 27 ga watan Disambar 2020.

Yanzu da ana jira aga irin hukunci da kotun za su yanke gam da manyan ‘yan takarar a zaben shugaban kasar da za’a yi.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG