Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Nijer: Kwamitin Dattawan Kasar Ya Bukaci Hadin Kan 'Yan Nijer


Kwamitin dattawan Nijer ya yi kira ga dukkan bangarorin da ke da hannu a sha’anin tsara zabe su dauki matakan da za su bada damar gudanar da komai cikin haske da adalci ba tare da nuna wa kowane dan kasa wariya ba.

Karo na biyu kenan cikin wata daya da kwamitin dattawan da hukumar kare hakkin bil'adama ta CNDH ta kafa ke jan hankalin masu ruwa da tsaki akan sha’anin zaben Nijer game da batun zaman lafiya, bayan la’akari da yadda bangarorin siyasa ke ci gaba da yi wa juna kallon hadarin kaji.

Shugaban hukumar ta CNDH Dr. Khalid Ikrit, shi ne jagoran wannan kwamiti, ya ce nauyi ne da ya rataya a wuyan kowane dan kasa ya bada gudummowar da za ta taimaka a gudanar da zabe cikin yanayin haske, adalci, da kwanciyar hankali ba tare da ware wani ko wasu ba.

Hukumomin shari’a, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da kuma jam’iyyun siyasa na dukkan bangarori, kungiyoyin kwadago, kungiyoyin kare hakkin jama’a da ma dukkan ‘yan kasa, na da rawar takawa wajen cimma gurin ganin an gudanar da wadanan zabuka ba tare da wata tashin-tashina ba, a saboda haka kwamitin na dattawa ya bukaci shugaban Nijer Issouhou Mahamadou ya dubi matsayinsa na jagoran al’uma ya ja kunnen 'yan kasar, kamar yadda mai shari’a Amadou Ali China, magatakardan hukumar ta CNDH ya bayyana.

Zaben na ranar 13 ga watan Disamban shekarar 2020 da wanda za a gudanar a ranar 27 ga watan na zuwa ne a wani lokaci da kasar Nijer ke fama da matsaloli da yawa inji shugaban kungiyar addinin Islama ta AIN, Cheik Djibiril Soumaila Karanta.

Mambobin kwamitin sun ce sun gudanar da wani zagayen da ya basu damar ganawa da shugaban hukumar zabe ta CENI, da shugaban majalisar sasanta rigingimun siyasa wato CNDP, da jam’iyyun adawa da masu rinjaye, da ministan cikin gida, da kungiyoyin kwadago domin ankarar da su halin rashin tabbas da suka ce ana ciki a Nijer, a saboda haka ya zama wajibi kowane dan kasa ya bada gudummowa don ganin wadannan zabukan sun gudana cikin kwanciyar hankali.

Saurara cikaken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Kudurin wasu 'yan Najeriya na sabuwar shekara a fannin lafiya, da wasu sauye-sauyen da suke fatan yi don samun nasara a rayuwarsu
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p

No media source currently available

0:00 0:05:16 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG