Muhimmancin wannan zabe ya sa duk bangarorin siyasar Nijer ke ikirarin shi zai yi nasara a fafatawar da za a yi ranar 27 ga watan Disamba.
Matakin bai wa dan takarar jam’iyyar PNDS mai mulki Bazoum Mohamed damar shiga wannan zabe a yayin da kotu ta yi watsi da takardun jagoran ‘yan adawa Hama Amadou saboda rashin cancanta ya sake farfado da mahawara a tsakanin magoya bayan ‘yan hamayya da masu mulki.
Kundin zaben jamhuriyar Nijer a sashensa na 137 ya ayyana cewa jam’iyyun siyasa na da ‘yancin maye gurbin ‘yan takararsu na farko idan bukatar hakan ta taso, sai dai wani masanin doka Dr. Maina Boucar Karthe, ya ce doka ta fayyace dalilan da ke bada damar aiwatar da irin wannan sauye-sauye.
A na su bangare masu rajin kare dimokradiya irinsu shugaban kungiyar Voix des sans Voix Nassirou Saidou, na cewa kula da batun mutunta ranakun zabe ita ce maganar da ya kamata a maida hankali akanta a wannan lokaci da aski ya zo gaban goshi.
Saurara karin bayani a sauti:
Facebook Forum