Sanin muhimmancin aikin sa ido a sha’anin zabe a kasashe masu tasowa irinsu jamhuriyar Nijar ya sa gamayyar kungiyoyin fararen hula ta COCEN hada gwiwa da kungiyar Tarayyar Turai wajen shirya wannan taro da ke hangen bin diddigin wadanan zabubuka da ake shirin gudanarwa cikin wani yanayi na rashin jittuwa a tsakanin ‘yan siyasa..
Shugaban gamayyar ta COCEN, Dambaji Son Allah, ya ce wannan taro da ke matsayin na farko a jerin tarurruka 3 da suke fatan tsarawa, wata gudunmowa ce da za ta taimaka a gudanar da zabubukan 27 ga watan disamba cikin yanayin lumana da kwanciyar hankali.
Kimanin jami’ai 750 ne COCEN ke fatan jibgewa a sassan daban daban na kasar Nijar domin aikin sa ido a runfunan zabe yayin da wasu 160 ke da alhakin fake halin da dimokradiyar wannan kasa ke tafiya ta yadda za a samu bayanai akai akai.
Jagoran hadakar kungiyoyin Reseaux Esperance, Malan Maman Bachar, ya ce wannan mataki na iya tasiri akan sha’anin gudanar da zabe.
Da ma dai masu daukan wannan horo na da kwarewa a fannin saka ido a sha’anin zabe saboda haka bayan kammala wannan zama zasu garzaya zuwa jihohi domin horar da takwarorinsu na karkara ta yadda za a saka ido kan wadanan zabubuka a kowane lungu da sakon Nijar.
Yanzu dai ana iya cewa aski yazo gaban goshi a game da shirye shiryen babban zaben kasar ta Nijar inda ake saran gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Lahdi 13 ga watan Disamba.
Sannan za a yi zaben ‘yan majalisar dokoki hade da zagayen farko na zaben shugaban kasa a ranar 27 ga watan nan abin da ya sa hukumar zabe soma kiran jam’iyyun siyasar da ba su aika wakilansu a hukumar ba su hanzarta aika mata sunayen mutanensu tun lokaci bai kure ba.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma: