Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gamsu Da Zaben Kananan Hukumomi a Nijar


Ofishin Jakadancin Amurka a Nijar
Ofishin Jakadancin Amurka a Nijar

Ofishin jakadancin Amurka a Jamhuriyar Nijar ya bayyana gamsuwa da yanayin da aka gudanar da zaben kananan hukumomi na ranar 13 ga watan Disamba a fadin kasar ta Nijar

Sai dai Ofishin ya gargadi mahukunta akan bukatar daukan matakai donganin ba a fuskanci matsaloli ba a zaben ‘yan majalisar dokokin kasa da na shugaban kasa da za a yi na ranar 27 ga watan.

A wata sanarwar da aka aikewa ‘yan jarida a washegarin zaben kananan hukumomin da ya gudana a Nijar ofishin jakadancin Amurka ya fara ne da jinjinawa al’umar wannan kasa saboda abin da aka kira halin dattakon da suka nuna a tsawon wunin na ranar Lahdi 13 ga watan Disamba.

Yayin da jami’an da suka sa ido suka ce sun gano wasu kura kuran da suka shafi tsare tsaren wannan zabe da aka gudanar.

Jami’in hulda da manema labarai a ofishin jakadancin Amurka a Nijar, Alhaji Idi Barau, ya ce an gudanar da wannan zaben cikin tsanaki, kwanciyar hankali da lumana, kuma har ila yau ma’aikatan ofishin jakanda cin Amurka masu saka ido sun gano a cikin tafiyar da harkar zaben sun lura da cewa duk da yake an yi zaben cikin kwanciyar hankali.

Ya kuma kara da cewa an gano wasu mazbu inda aka samu matsaloli da suka hada da rashi isar kayan zabe da wuri da kuma bude rumfunan zaben.

Kana kuma sun yi kira da hukumar zaben da ta gyara inda aka samu kurakurai a zaben ‘yan majalisa da na shugaban kasa da za a yi a karshen watan Disamba.

Gwamnatin Amurka ta hanyar wannan sanarwa ta bukaci masu alhakin tsara zabe su dauki matakan da zasu taimaka a kaucewa afkuwar irin matsalalolin a zabubbukan da ake shirin gudanarwa a ranar 27 ga wannan wata.

Karancin matakan kare kai daga cutar corona da ma rashin daukar wadanan matakai a galibin runfunan zabe na daga cikin abubuwan da aka gano a yayin gudanar da zaben na ranar 13 ga watan Disamba.

Kasar Amurka ta sake tunatar da hukumomin Nijar mahimmancin mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki da ‘yancin gudanar da taro da dukkan ‘yancin dan adam da abubuwan da dimokradiyya ta yi tanadi ga ‘yan kasa.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG