Sanin rikicin da ke tattare da sha’anin zabe a kasashen Afrika, inda a sau tari ‘yar karamar magana ke rikidewa ta zama tashin hankali, ya sa Majalisar Dinkin Duniya da wasu manyan kungiyoyin kasa da kasa suka shirya babban taron, domin tunatar da ‘yan siyasar kasar muhimmancin zaman lafiya a daidai wannan lokaci da kasar ke tunkarar babban zabe.
Manzo na musamman na a Majalisar Dinkin Duniya a yankin Afrika ta yamma Dr. Mohammad Ibn Chambas ya ce, babban nauyi ne, kuma ya rataye a wuyan ‘yan siyasa domin dorewar yanayin zaman lafiya.
Ya kuma ce akwai a mayar da hankali wajen darajanta juna da musayar yawu akan gaskiya, wani abu ne da zai taimaka a fahimci juna a yayin gudanar da wadanan zabubbuka.
Mutunta ka’idodi shi ne kadai hanyar da ta zama dole a bi wajen warware kowane irin rikicin zabe.
Sarakunan gargajiya na da rawar takawa a ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasa, saboda haka aka bukaci gudunmuwarsu don ganin an cimma burin da aka sa gaba a karkashin wannan taro.
Sarkin Tsibirin Dogon Doutsi mai martaba Samna Boubacar Marafa ya yaba da wannan tsari.
Wasu daga cikin ‘yan takara sun amsa wannan gayyata ta MDD da nufin jaddada goyon baya ga wannan yunkuri.
Dr. Souleyman Abdallah, dan takarar jam’iyar NIGERINA, ya ce, sun gamsu da irin wannan taron, kuma suna fatan za a yi zaben lafiya.
Kungiyoyin mata sun sha alwashin ci gaba da ba da shawarwarin da aka tsayar a wannan taro zuwa sassan kasa ta yadda za a kare matasa daga bangar siyasa aikin da shugabar kungiyar CONGAFEN Madame Kako Fatima ta ce, yana bukatar samun hadin kan kowa.
A bara Majalisar Dinkin Duniya ta shirya makamancin wannan taro a Najeriya gabanin zabe, domin riga kafin barkewar rigingimu masu nasaba da zabe, haka kuma an yi irin wannan zama a jajibirin zaben Burkina Faso wanda aka yi a ranar lahdi 22 ga watan Nuwamba.
Kyakkyawan sakamakon da aka samu a karkashin wannan tsari ya sa MDD shirya irinsa a Nijer, wanda kuma nan ba da jimawa ba ake saran gudanar da makamancinsa a Ghana don ganin zabubukan da wadanan kasashen ke shirin gudanarwa a watan gobe an yi su salum alum.