Daruruwan motoci da suka tashi daga kasashen Ghana da Togo dauke da lodi akan hanyarsu ta zuwa Nijar na can jibge a kan iyakar Burkina Faso, inda su ke jiran samun rakiyar jami’an tsaro sakamakon lalacewar al’amuran tsaro.
Wasannin motsa jiki na daga cikin jerin abubuwan da suka fara jan hankulan masu bukata ta musamman a ‘yan shekarun bayan nan a kasashen Afrika
Jam’iyyun hamayya a jamhuriyar Nijar sun dukufa wajen tayar da magoya bayansu daga barci don ganin sun yi nasara a zaben mutanen da za su wakilci ‘yan kasar mazauna kasashen waje a majalisar dokokin Nijar.
Wata kungiyar kasar Amurka da ake kira Health and Development International ta sanar cewa jamhuriyar Nijer ta samu nasarori a yunkurin magance matsalar yawan matan da ke mutuwa sanadiyyar zubar da jini a yayin nakuda.
A makon jiya mun duba yadda Achirou Salissou Almou, wani mai nakasa dake Maradi a Jamhuriyar Nijar, ya jingine aikin kere-keren kayayakin fata da kanikancin babura ya shiga sana’ar daukar hoto.
A jamhuriyar Nijer lalacewar al’amuran tsaro na ci gaba da kara yawan makarantun dake rufe kofofinsu a jihar Tilabery mai iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso lamarin da ke shafar karatun yara sama da 70000.
A jamhuriyar Nijer ‘yan siyasa na bangarori daban daban sun bayyana kyaukyawan fata ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu wanda ya yi rantsuwar kama aiki a jiya litinin 29 ga watan mayun 2023.
Hukumomi a jihar Tilabery sun gargadi kungiyoyin agaji su yi takatsatsan da wasu daga cikin hanyoyin zirga zirga da bayanai suka tabbatar da cewa suna da matukar hadari sanadiyyar tsanantar aika aikar ‘yan ta’adda.
A kashi na farko na wannan hira da Mansour ya yi mana bayani dangane da yadda aka yi ya tsinci kansa a halin nakasa.
Kasar Amurka ta bayyana shirin bayar da tallafin CFA miliyan 1,600 a matsayin gudummowar da za a zuba a asusun bai daya na samar da takin zamani ga mazaunan karkara a jamhuriyar Nijar.
A yayin da kotun tsarin mulkin kasa ta Jamhuriyar Nijar ta bayyana sunayen jam’iyu 10 da suka cancanci shiga zaben wakilan ‘yan kasar mazauna ketare a majalisar dokoki, hukumar zabe ta CENI ta dukufa kan ayukan isar da katuna da kayayyakin zabe zuwa kasashen da ya kamata a gudanar da wannan zabe.
A jamhuriyar Nijar shugabanin kungiyar ‘yan tawayen UFPR sun ba da sanarwar ajiye makamai bayan da suka gana da shugaba Mohamed Bazoum a fadarsa a karshen mako.
Majalisar dokokin jamhuriyar Nijar ta amince da dokar tsawaita shekarun ritayar ma’aikatan gwamnati, matakin da kungiyoyin kwadago suka yi na’am da shi yayin da su kuma matasa ke ganin abin tamkar wani shingen da zai hana su samun aiki da wuri.
A jamhuriyar Nijar, a karo na biyu a kasa da mako daya hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kama wasu mutane dauke da tan kusan daya na tabar wiwi a lokacin da suka yi kokarin tsallaka kogin Kwara da ke yankin iyakar Nijar da jamhuriyar Benin da ma Najeriya.
A jamhuriyar Nijar gamayyar kungiyoyin fafutuka ta M-62 ta shigar da bukata a hukumar yaki da cin hanci, ta gurfanar da tsohon shugaban kasar Mahamadou Issouhou a gabanta.
A jamhuriyar Nijar wasu jami’an tsaron kasar sun mutu bayan da motarsu ta taka nakiya lokacin da suke aikin sintiri a jihar Tilabery mai fama da aika-aikar ‘yan ta’addan da ke da sansannoni a kasashen Mali da Burkina Faso.
Dalibai kimanin 47 da suka makale a Sudan sun sauka birnin Yamai a cikin daren laraba bayan da suka shafe kwanaki uku a tsakanin biranen Khartum da N’Djamena, suka ratsa ta Angola kafin su isa gida cikin wani jirgin da gwamnatin Nijer da tura kasar Tchad.
A cikin shirin na wannan makon, rashin ayyukan yi ko jarin tsira kasuwanci wata matsala ce da ke daga hankulan masu bukata ta musamman a Ghana.
Domin Kari