Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Tsaro Na Sanya Ana Kara Rufe Makarantu A Jihar Tilabery


Wata Makaranta A Jihar Tilabery
Wata Makaranta A Jihar Tilabery

A jamhuriyar Nijer lalacewar al’amuran tsaro na ci gaba da kara yawan makarantun dake rufe kofofinsu a jihar Tilabery mai iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso lamarin da ke shafar karatun yara sama da 70000.

Wannan ya sa ‘yan fafutika ke nuna damuwa saboda a cewarsu abu ne da zai iya yin mugun tasirin akan makomar dubban yara.

Sama da makarantu 100 ne aka gano cewa sun karu akan wadanda ke rufe a watan oktoban 2022 a jihar Tilabery sanadiyar matsalolin tsaro.

An gano hakan ne a karshen rangadin da ministan ilimi Pr Ibrahim Natatou ya gudanar a wannan yanki daga ranar 23 zuwa 28 ga watan Mayun 2023.

Babban jami’in a sashen kula da al’amuran karatu a yankunan dake cikin dokar ta baci a ofishin ministan ilimi Malan Attahiou Sabra ya yi mana karin bayani. Ya ce an rufe makakarantu da dama a wasu yankuna saboda matsalar tsaro kuma yawancinsu na so su bude amma suna gudun kar su bude kuma su jawo wa kan su bala'i.

Ganin yadda wannan matsala ke zama barazana ga makomar yara da kuma irin illolin da abin ka iya haddasa wa zamantakewar al’umma ya sa ‘yan rajin kare hakkin dan adam nuna damuwa a kai. Son Allah Dambaji shine shugaban gamayyar kungiyoyin hakkin dan adam ta ROADD.

To sai dai hukumomin ilimi na cewa akwai alamun nasara a tsarin nan na cibiyoyin karantarwa na musamman da aka bullo da shi a farkon shekarar karatun da muke ciki inda ‘yayan ‘yan gudun hijirar cikin gidan jihar Tilabery ke samun ilimi.

Karancin jami’an tsaro da rashinsu a wasu sassan jihar Tilabery na daga cikin dalilan da wasu majiyoyi suka ayyana a matsayin wadanda ke bai wa ‘yan ta’adda damar cin karensu ba babbaka a yayin da barayi da ‘yan fashi ke fakewa da yanayin da ake ciki a kasashen Mali da Burkina Faso don tafka ta’asa akan al’umomin garuruwan iyakokin kasashen nan 3 da ke arcewa akai akai domin neman mafaka a wuraren da ke da tsaro a jihar ta Tilabery da jihar Tahoua.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG