Dalibai da iyayen wadanda aka dawo da su daga kasar Sudan sun bayyana gamsuwa da yadda gwamnatin kasar ta dauki matakin gaggawa na dawo da su gida bayan sun fice daga Sudan inda ake fama da tashin hankali.
A hirar shi da manema labarai jim kadan bayan isowarsu, Ahmed Rabe Kane daya daga cikin dalibai, ya bayyana irin wahalar da suka sha a hanya, yayinda ya ke nuna godiya ga gwamnatin Jamhuriyar Nijar sabili da dawo da su gida.
Ahmed ya kara da cewa, a karkashin wani tsarin hadin guiwar hukumomin Nijer da na Tchad ne aka kwashe su daga jami’ar Khartum zuwa N’Djamena cikin jirgin kasar bayan da wakilin Nijer a Sudan ya gudu ya bar su cikin tashin hankali.
Bisa ga bayaninsa, lokacin da suka isa N’Djamena sun sami kyaukyawan tarba daga jakadan Tchad na Sudan wanda ya basu masauki da abinci. Ya kuma bayyana cewa, sun yi tafiya ta tsawon kwanaki fiye da 3 a kan hanya daga khartum kafin su isa kasar Tchad bayan sun ratsa ta Angola.
Ahmed ya bayyana cewa, abinda ya burge shi shine, yadda cikin kankanen lokacin bayan da suka buga waya gida Nijer shugaban kasa ya tura jirgin sama mai tutar Nijer zuwa N’Djamena inda kai tsaye aka kwashe su zuwa birnin Yamai.
Sai dai a yayinda ake murnar zuwan wadanan dalibai, kusan sai a ce murna ta koma ciki sakamakon rasuwar daya daga cikin daliban da ya rasu akan hanya, wanda kuma aka yi jana’izarsa a da rana a birnin Yamai .