Tun a shekarar 2020 ne ya kamata ‘yan Nijar mazauna ketare su aiko da wakilai a majalisar dokokin kasar, sai dai hakan ba ta samu ba sanadiyar annobar COVID-19.
Dalili kenan bayan la’akari da yadda aka sami lafawar wannan cuta ya sa hukumar zaben Nijar ta CENI ta bukaci ‘yan kasar da ke zama ketare su je rumfunan zabe a ranar 18 ga watan Yuni na 2023 don kada kuri'a.
Dubban ‘yan Nijar da ke zaune a kasashen waje ne suka yi rajista albarkacin zaben na ranar 18 ga watan Yuni, wanda kuma ke matsayin na cike gurabe a majalisar dokokin kasar mai mambobi 171, abin da ya sa jam’iyyun adawa suka dage haikan don ganin sun yi galaba a wannan fafatawa da suke dauka da muhimmanci.
Jam’iyyar RDR Tchanji, wacce ke daya daga cikin jam’iyyun da kotun tsarin mulkin Nijar ta yi watsi da takardun ‘yan takararta, ta yi kiran magoyanta da su zabi ‘yan takarar madugun jam’iyyar hamayya ta Moden Lumana, ta Hama Amadou.
"Ya ku magoya bayan jam‘iyyar RDR maza da mata mazauna kasashen waje, da ni da uwar jam’iyya mun sani ba wata tantama za ku kada wa ‘yan takarar Moden Lumana kuri’un da zasu basu damar yin nasara a zaben 18 ga watan Yuni, a cewar tsohon shugaban Nijar Alhaji Mahaman Ousman kuma shugaban RDR Tchanji,
Ya kara da cewa, kamar yadda ku ka sani, mu na da dadaddiyar hulda da wannan jam’iyya wacce ta kafu a karkashin turbar amana da yarda da juna da nufin tabbatar da adalci da gaskiya da hada kan ‘yan Nijar."
Wannan kira da ke zuwa a wani lokaci da yakin neman zabe ya kankama, dama ce da RDR Tchanji ke amfani da ita don yi wa Moden Lumana godiya da goyon bayan da ta bai wa Mahaman Ousman a zaben da ya zo na biyu a jerin wadanda suka nemi shugabancin Nijar a watan Disamban 2020.
Hakan ne ya sa RDR Tchanji aike wa da tawagogi zuwa kasashen waje domin taya Moden Lumana neman yardar ‘yan kasar mazauna ketare, a cewar wani jigo a jami’iyyar RDR Tchanji Ibrahim Manzo.
Zaben wanda ke matsayin na samar da kujeru 5 na wakilcin majalisar dokokin Nijar zai gudana a kasashe 15 wadanda suka hada da 12 na nahiyar Afrika, kasashe 2 na Turai, sai kuma Amurka. Jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki wacce ita ma ke fatan ganin ta taka rawar gani a fafatawar ta ranar 18 ga watan Yuni, ta aike da tawaga zuwa kasashen waje a karkashin jagorancin shugabanta na kasa Foumakoye Gado da nufin yakin neman zabe.
Saurari rahoton cikin sauti: