Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kara Tsawaita Tallafin Shirin MCC Don Samar Da Wadatar Taki A Nijar


Bukin Tsawaita Tallafin MCC Don Samar Da Wadatar Taki A Nijer
Bukin Tsawaita Tallafin MCC Don Samar Da Wadatar Taki A Nijer

Kasar Amurka ta bayyana shirin bayar da tallafin CFA miliyan 1,600 a matsayin gudummowar da za a zuba a asusun bai daya na samar da takin zamani ga mazaunan karkara a jamhuriyar Nijar.

Wannan shi ne zagaye na uku da Amurka ke bada irin wannan tallafi a karkashin shirinta na Millenium Challenge Corporation da ake kira MCC a takaice, da nufin sassauta wahalhalun manoma a Nijar.

BukinTsawaita Tallafin MCC Don Samar Da Wadatar Taki A Nijer
BukinTsawaita Tallafin MCC Don Samar Da Wadatar Taki A Nijer

Mataimakin shugaban shirin Millenuim Challenge Corporation Mr. Cameron Alford, ya yi jawabi a yayin wani kwarya-kwaryan biki da aka shirya a gidan jakadan Amurka da ke birnin Yamai.

Mr. Cameron ya yi albishir game da sabon tallafin kudaden takin zamanin da kasar Amurka ta yanke shawarar bayar wa domin ci gaban shirinta na samar da taki akan farashi mai rangwame a Nijar.

Bukin Kara Tsawaita Tallafin MCC Don Samar Da Wadatar Taki A Nijer
Bukin Kara Tsawaita Tallafin MCC Don Samar Da Wadatar Taki A Nijer

"Ina farin cikin sanar da cewa shirin MCC zai zuba miliyan 1,600 na CFA a zagaye na gaba na tallafin takin zamani domin manoman Nijar. Iyali 35,000 ne muke shirin bai wa tikitin da ke bada damar karbar wannan tallafi a yayin ayyukan noman da ake shirin farawa nan gaba.

Gwamnatin Nijar wacce ta kafa asusun bai daya da zummar samar da wadatar taki kuma akan farashi mai sauki, ta yaba da gudummowar shirin MCC a wannan sabuwar tafiya da ke hangen bunkasa noma a karkashin shirin ‘Yan Nijar su ci da ‘yan Nijar.

Yahaya Garba, shi ne magatakardan ofishin ministan noma na Nijar, ya ce sun yi murna da tallafin takin saboda a baya gwamnati ce ke saidawa amma yanzu ya koma hannun yan kasuwa. Tallafin dai zai sa a samu taki mai rahusa.

Bukin Kara Tsawaita Tallafin MCC Don Samar Da Wadatar Taki A Nijer
Bukin Kara Tsawaita Tallafin MCC Don Samar Da Wadatar Taki A Nijer

Wannan shi ne zagaye na uku da manoma ke karbar tallafin kudaden taki a karkashin shirin MCC, wadanda suka mori wannan shiri a zagayen farko da na biyu sun ga sauyi a gonakinsu.

Saouda Tinni, wata dattijuwa da ke noman shinkafa, ta yaba da tallafin. Tana mai cewa a lokacin da babu wannan shiri ba su da abin yi.

"Ni ba na fankasu ba na tuyar kosai, noma na sa gaba, da shi nike biya wa yarana kudin karatu kuma da shi nike masu kayan Salla da dukkan wasu bukatu. A tsawon shekarun nan biyu na karbi gonata daga hannun wadanda na ba jingina, na gode Allah, a cewar Saouda.

Ta kara da cewa duba ka gani yanzu har waya na mallaka ina kiran yarana da ita, alhali a shekaru 6 na baya zaune nake ba aiki.

A yayin bikin kaddamar da wannan zagaye na uku na kudaden tallafin takin na shirin MCC, an sanar cewa tsarin ya taimaka wajen magance tsadar taki da duniya ke fuskanta sanadiyar mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

A gefe guda kuma, a ranar Laraba 17 ga watan Mayu aka damka wa gwamnatin Nijar hanyar motar Dosso Bela a hukumace, wace kasar Amurka ta dauki dawainiyar gyaranta a karkashin shirin na MCC.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

XS
SM
MD
LG