Kawo yanzu hukumomi ba su yi karin haske game da faruwar lamarin ba yayin da mazauna yankin ke kara nanata kiran neman mafita.
Lamarin ya faru ne a jiya lahdi 7 ga watan Mayun 2023, a kauyen Samira mai arzikin ma'adanin zinari da ke jihar Tilabery, inda motar jami’an tsaron garde Nationale ta taka nakiyar da ake hasashen mayakan kungiyar IS ne suka dasa ta a wani bangare na sabon salon yakin da suka kaddamar a ‘yan makwannin nan a yankunan Diffa da Tilabery masu fama da matsalolin ta’addanci.
Majiyoyi sun bayyana cewa 7 daga cikin jami’an tsaro da wannan tsautsayi ya fadawa sun rasa rayukansu, amma kuma ba'a bayyana yawan wadanda suka ji rauni ba.
Ibrahim Mamoudou wani dan fafutuka ne a jihar Tilabery kuma ya tabbatar wa Muryar Amurka cewa lallai an samu hatsarin sojoji da suka fada bisa wata nakiya a yayin da suke hanya zuwa a kauyen Samira mai arzikin karfen zinare dake jihar Tilabery.
Koda yake a watannin bayan nan ana ganin alamun samun saukin hare-haren da aka yi fama da su a jihar ta Tilabery, abubuwan da ke wakana a halin yanzu a kasashe makwafta na haifar da fargaba a zukatan mazaunan yankin, wadanda ke ganin akwai bukatar kara karfafa matakai don gudun komawa ruwa.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto hukumomi ba su yi wani bayani ba game da abin da ya faru ga jami’an tsaron a kauyen na Samira.
To amma a daya gefe, sanarwar mako biyu da ma’aikatar tsaron Nijer ta fitar a ranar Juma’ar da ta gabata ta ce askarawan kasar sun kashe ‘yan ta’adda 6 tare da kama wasu 19 da motoci 2 da tarin manyan bindigogi a yammacin garin Ayorou na jihar Tilbaery, yayin da wasu ‘yan bindiga 3 suka sheka lahira lokacin da suke dasa nakiyoyi a kudancin jihar Diffa mai fama da ayukan Boko Haram.
Saurari rahoton a sauti: