A shirye shiryen fara amfani da sabuwar fasahar 5G a Najeriya, a jiya ne kamfanonin sadarwar wayar salula biyu wadanda suka hada da MTN da MAFAB suka yi nasarar samun gwanjon lasisin fasahar.
La’akari da yanda arewacin Najeriya ke cikin halin ha’ula’i sakamokon cigaba da tabarbarewar tsaro da yankin ke fuskanta musamman a cikin sati biyu da suka gabata, mata masu fafatuka sun ce kowa ya kare kansa.
Yayin da Najeriya ke ci gaba da fama da karancin likitoci, sai kuma ga shi hukumar kula da harkokin likitocin kasar ta ce wadanda su ka karanta likitanci a kasashen waje za su biya sama da Naira miliyan guda don kwasa-kwasai na samun lasisin aikin likita a kasar.
Hukumar EFCC ta ce ta sami rahoton kwamitin bincike na rundunar soja daga shekarar 2007 zuwa 2015 inda biliyoyin naira na sayen makamai suka salwanta.
'Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar hana su shiga wasu kasashe, ciki har da Burtaniya, sakamakon bullar nau’in cutar covid 19 na Omicron.
Najeriya ta shiga jerin kasashe 12 a fadin duniya da aka samu bulluwar sabon nau’in cutar coronavirus da ake kira Omicron. Nau’in cutar da aka gano a kudancin nahiyar Afrika ya shigo Najeriya ne ta hanyar wasu matafiya biyu da suka zo kasar daga Afrika ta kudu.
Ana sa ran taron zai ba Najeriya damar kulla kawance mai ma’ana da kasashe sama da 190 a fadin duniya da suka halarci taron na kwanaki uku a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana sabon nau'in cutar Korona na Omicron a matsayin "hadari mai girma" a duniya
Ma’aikatar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya ta sanar da cewa zuwa watan Afrilun badi ake sa ran jirgin saman kasar zai fara aiki.
Kungiyar matan shuwagabannin kasashen nahiyar Afrika kan zaman lafiya ta gudanar da taron yini guda karo na 9 wanda uwargidan shugaban Najeriya Aisha Muhammadu Buhari ta karbi bakuncinsa a wannan karon a birnin tarayyar kasar Abuja.
Mawakin ya yi kudurin gwada farin jininsa a kafafen sada zumunta, ta hanyar neman tarbacen kudi Naira miliyan 100, amma ya kai ga samun har Naira miliyan 200.
Kasar Aljeria ,Comoros, cuba da Nicaragua Suna cikin jerin kasashen na musammam da aka sa musu ido sakamokon yanda gwamnatocinsu ke taka rawa wajen taka yancin addini.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta duniya Amnesty International, ta bayyana cewa gazawar gwamnatin Najeriya wajen shawo kan matsalar fyade da sauran laifuka na cin zarafin mata da kananan yara na kara ta’azara sakamokon rashin hukunta masu aikata laifin.
Ana sa ran wannan shiri zai taimaka wajen bai wa mata damar fitowa su bayyana kowanne irin cin zarrafi su ke fuskanta a rayuwa.
Domin Kari