Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Cire Najeriya Daga Cikin Kasashe Masu Take ‘Yancin Addini


Buhari Da Blinken.
Buhari Da Blinken.

Kasar Aljeria ,Comoros, cuba da Nicaragua Suna cikin jerin kasashen na musammam da aka sa musu ido sakamokon yanda gwamnatocinsu ke taka rawa wajen taka yancin addini.

Kasar Amurka ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashen da ta ce suna tauye 'yancin yin addini a kasashensu.

A cikin wata sanarwa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fitar, ya lissafa kasar Saudiyya, Rasha, China, Pakistan, Burma, Turkmenistan da wasu kasashe, a zaman sabon jerin kasashen da ke tauye hakki da yancin addini na shekarar 2021.

A shekarar 2020 ne Amurka ta saka Najeriya da wasu kasashe shida a jerin kasashen da ke tauye hakkin masu addini ko kuma rashin daukan matakan kare masu addinin.

Blinken, wanda a yanzu yana kasar Kenya da ke Gabashin Afirka don ziyarar aiki, zai karaso Najeriya don ganawa da shugaba Muhammadu Buhari da wasu jami'an gwamnatinsa.

Sakataren na harkokin wajen Amurka, a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba ya ce: "Amurka ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin ta na kare hakkin masu addini a kowace kasa."

Blinken ya ce gwamnatin Amurka za ta cigaba da saka takunkumi kan kasashe da gwamnatocin da ke hana 'yan kasarsu 'yancin yin addinin da suke so.

A na sa ran Blinken zai yi cikekken bayanani idan ya iso Najeriya kan cutar Covid 19 da hanyoyin gina tattalin arzikin duniya da yaki da matsalar yanayi, da farfado da tsarin dimokuradiyya, da kuma inganta zaman lafiya da tsaro.

XS
SM
MD
LG