Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun 'Yan Awaren Kasar Kamaru Sun Kashe Mutane 11 A Jihar Taraba


Yan bindiga.
Yan bindiga.

Daruruwan mazauna karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba sun arce daga yankin bayan da dakarun 'yan awaren kasar Kamaru suka kai masu farmaki, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 11, ciki har da wani basarake da aka kashe a masarautarsa

Wannan lamari ya auku ne a jiya Laraba 17 ga watan Nuwamba, inda mayakan 'yan awaren su ka kona gidaje da makarantu da dama sannan suka yi awon gaba da kayayyaki.

A hirar da gidan talabijin na Channels ya yi da wani Joseph Manga wanda ya ke dan’uwa ne ga basaraken da aka kashe kana mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Darius Ishaku, ya tabbatar da lamarin inda ya ce sojojin Ambazoniya sun fara kai hari a kan iyakar kasar Kamaru kafin su tsallaka zuwa Najeriya domin tayar da tarzoma.

Ya kuma kara da cewa dakarun sun fara shiga fadar dan’uwansa suka kashe shi kafin su kashe sauran mutanen.

Shugaban karamar hukumar Takum, Shiban Tikari, ya ce an gano gawarwakin mutane biyar da aka kashe sannan har yanzu ba a ga wasu da dama ba.

Shugaban ya kara da cewa an tura sojoji daga karamar hukumar Takum don kare al’umomin da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.

Jariyar Daily Trust ta ruwaito cewa a watan da ya gabata sojojin Kamaru sun fatattaki al’umomin iyakoki uku a karamar hukumar Kurmi da ke jihar, bayan sun fake da neman 'yan awaren Ambazonia

A zaman majalisar dattawan Najeriya na jiya Laraba, dan majalisar mai wakiltar mazabar Taraba ta Kudu kana shugaban marasa rinjaye a majalisar Emmanuel Bwacha, ya ce farmankin da 'ya awaren na Kamaru suka kai ya yi sanadiyar tsarewar mazauna kyauyen da ke da nisan kilomita 20 daga madatsar ruwa ta Kashimbilla

Yankin karamar hukumar Takum na kan iyakar jihar Taraba da Jamhuriyar Kamaru

XS
SM
MD
LG