Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Ta Gurfanar Da Tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya Da Wasu Janar 2 A Kotu Bisa Zargin Badakalar Naira Biliyan 13


EFCC
EFCC

Hukumar EFCC ta ce ta sami rahoton kwamitin bincike na rundunar soja daga shekarar 2007 zuwa 2015 inda biliyoyin naira na sayen makamai suka salwanta.

Hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya, EFCC ta gurfanar da tsohon babban hafsan sojan kasa Laftanar Janar Kenneth Minimah gaban babbar kotun birnin tarayya, bisa zargin almundahanar kudade.

EFCC ta gurfanar da Minimah ne tare da tsohon shugaban sashen bayanai da kasafin kudi na soja Manjo Janar A.O Adetayo, da kuma tsohon shugaban sashen kudi na soja Burgediya Janar R.I.Odi kan badakalar Naira biliyan 13 na sayo makamai.

Wadanda a ke tuhumar sun nuna har yanzu suna karkashin kulawar rundunar soja don haka in ma da wani abu da a ke zarginsu, to sai dai a koma ga rundunar soji don ta duba da daukar matakin tafiya kotu.

Hukumar EFCC ta ce ta sami rahoton kwamitin bincike na rundunar soja daga shekarar 2007 zuwa 2015 inda biliyoyin naira na sayen makamai su ka salwanta.

Hukumar ta kuma kara da cewa kudin sun zurare zuwa asusun wasu sassa da sam ba su da alaka da rundunar soja wanda hakan ya kawo gagarumar asara.

Kotun ta ba sassan wa'adin kwana 21 su gabatar da bayanan su.

Ko da ya ke wannan ba shi ne karon farko da ake samun irin wannan badakalar kudade ba.

Idan za’a iya tunawa an taba tuhumar tsohon shugaban ma’aikatan sojin sama kana tsohon shugaban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Alex Badeh da badakalar kudade, wanda ana kan gudanar da shari’arsa ne ya hadu da ajalisa sakamokon harin wasu yan bindiga a watan Disambar shekarar 2018

XS
SM
MD
LG