Da ta ke jawabi a yayin karbar manyan baki da suka samu halartar taron a madadin gwamnatin tarayyar Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta bayyana muhimmacin aikin dake gaban matan shugabanin Afirka wajen cimma manufar da aka assasa kungiyar akai na samar da kariya da takaita tashe tashen hankula da kuma tallafi ga mabukata.
Ta ce ‘’muhimin aikin da kungiyar matan shugabanin Afirka kan zaman lafiya ta sa a gaba ya bayyana irin aikin da ke gaban mu a matsayin matan shugabanni, don haka hada wannan taro ya zo akan lokaci kuma shaida ce da ke nuni da cewa shugabancin da mu ke yi ya tabbatar da mu a matsayin jakadun mata da kuma nahiyar Afirka.’’
An kafa kungiyar ne tun a shakarar 1997, da nufin samar da zaman lafiya da tunkarar hanyoyin rage rikice rikice da nahiyar Afirka ke fuskanta, a karkashin jagorancin shugabar kungiyar ta farko uwar gidan mariyagayi Sani Abach, wato Maryam Sani Abacha.
Fatima Maada Bio, uwar gidan shugaban kasar Saliyo ta jinjinwa Hajiya Aisha Buhari bisa namijin kokarin da ta yi na karbar taron kungiyar, tana mai cewa aikin shi ne mu taimakawa ayyukan mazajenmu na cika burikansu akan al’ummarsu, mun zo nan ne dan mu tallafa mata bisa kiranmu da ta yi a matsayinmu na ‘yan uwa hakan ya kamata muyi. Don idan muna tare mun fi karfi, idan mu ka rabu kuma za’a samu matsala.
Hajiya Mairo Almakura da ke zama mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa dake bada shawara kan al’amuran kungiyar kasashen Afirka ta yi kari da cewa, an yi zaben shugabar kungiyar kuma aikin na da muhimmanci wajen hada kan kasashen Afrika saboda mata da yara su tashin hankali ya fi shafa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa muhimmacin wannan kungiya ya na kan manufarta na cewa batun samar da zaman lafiya ya zama babban abu da ke shafar duk wani cigaba a yankuna da dama a Afirka, ayyuakan ta’addaci sun samar da gibi mai yawa ga talauci, ba abin mamaki bane mata sune wadanda suka fi fuskantar tashin hankali a sanadiyar rashin zaman lafiya, don haka a tsayin ku na mata ina da tabbacin cewa kuna kan matsayin da za ku kawo zaman lafiya da kuma matakan da suka kamata.
Daga cikin matan shugabannin kasashen Afirka da suka samu halartar taron sun hada da matar shuganban kasar Ghana, Laberiya, Nijar, Namibiya Zimbabwe, Cote D`voire da sauran wakilan sauran kasashen nahiyar Afirka. A karshe dai an ba Hajiya Aisha Buhari matsayin shugabar Kungiyar da zata rike jagorancinta na tsawon shekaru biyu.
Saurari rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.