Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk Jam’iyyar Da Ke Son Nasara Dole Ta Rungumi Matasa - Saliu Mustapha


Alhaji Saliu Mustapha Dan takarar shugaban jamiyyar APC.
Alhaji Saliu Mustapha Dan takarar shugaban jamiyyar APC.

A yayin da gangar siyasa ta fara kadawa a Najeriya jam'iyya mai mulki a kasar wato APC tana kara shiga rudani, inda ake kara samun rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yayanta. To sai dai duk da haka sun amince da abu guda, wato sanin cewar tafiyar bata yuwuwa sai da matasa

Dan takarar shugabancin jami’yyar Saliu Mustapha ya shaida cewan a yayin da jam'iyyun adawa ke ba wa matasa shugabanci a bangare na matasa, su kuwa manyamanyan mukamai za a bai wa matasan.

Ya kuma ce ba wai ba a yaba da abun da dattijai a jam’iyyar suka yi ba ne amma lokaci yayi da matasa zasu ja ragama,

Ya ce sama da kashi 70 na kuri’un kasar na zuwa ne daga matasa. Don haka me ya sa za a bar su a baya?

Wannan jawaban na shi na zuwa ne adaidai lokacin da su kansu matasan jam’iyyar ta APC ke cewar dole wannan karan a dama da su, suka ce dukka shugabanin Najeriya da suka gabata mafi yawansu matasa ne a lokacin da suka rike ragamar, don haka yanzu me yasa ake cewa matasa ba za suyi ba.

Suka kara da cewa an gode da gudunmawar da dattijai suka bayar, amma dole a tafi da zamani a ba matasa damar su rungumi makomarsu da hannunsu.

Duk wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ‘yan aware daga jam’iyyar suka ce ba su yarda da jagorancin rikon jamiyyar ba, suka ce sun rusa jagorancin rikon kwaryar sun kuma nada nasu sabbi.

A saurari Rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG