Tuni muka fara gudanar da bincike a kan jami'an gwamnati da sunayensu ya fito a leken asirin Pandora Papers- Farfesa Mohammad Isah
Bayanan hakan ya fito bayan kammala taron wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya jagoranta a Abuja.
A yayin da farashin Dala ke ci gaba da tashi a kasuwanin bayan fage na Najeriya sakamakon matakin daina ba ‘yan canji kudi da babban bankin kasar ya dauka, darajar Naira na ci gaba da faduwa.
A kokarin da ta ke yi na wayar da kan al’umma kan muhimmacin yaki da cutar sankara a Najeriya a duk shekara cikin watan Oktoba, gidauniyar MEDICAID mai zaman kanta ta gudanar da wani tattaki a garin Abuja don fadakar da al’umma game da illar cutar tare da ba da tallafi ga masu fama da ita a kasar.
Gwamnatin Najeriya ta jaddada aniyarta na aiwatar da manufofi da shirye-shirye da za su inganta kasuwanci na fasahar zamani domin bunkasa kananan sana’oi a tsakanin matasa, musamma daliban da ke manyan makarantu.
Matsayar haka ta biyo bayan kudirin da sanata mai wakiltar Sokoto ta Gabas, Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir, da wasu takwarorinsa takwas suka gabatar a gaban majalisar.
Ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta yi amfani da karfin yawa da kwazo- matasa wajen rage hasturan matsalar tsaro a kasa.
Ma’aikatar Ilimi ta tarayyar Najeriya ta yi kira da dukkan masu masu ruwa da tsaki da su hada kai domin yaki da jahilci a fadin kasar.
Bayan kashe dan sandan, yan bindigar sun tafi da mutane 7 a unguwar Laka, ciki har da matar dan sandan da suka kashe da 'yarsa guda daya.
A wani bangare na taimakawa gwamnatin Najeriya shawo kan tarin mastalolin da suka addabi kasar musamman a fannin tsaro, hukumar wayar da kan al’umma ta kasa wato National Orientation Agency ta kaddamar da wani sabon kamfe.
Kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya sun zuba jarin sama da Naira Biiyan 500 don inganta ayyukan hukumar NADDC
Cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya NCDC ta fitar da sanarwar sabon adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus da yawansu ya kai 1,149, adadi mafi yawa da kasar ta taba samu a rana guda tun daga watan Feberu.
A cewar shugaban kwamitin shirye shirye na bikin Shehu Ahmed za’a kafa tarihi a ranakun Juma’a da Asabar a karamar hukumar Bichi inda za’a daura auren dan shugaban kasa da yar'sarkin garin da kuma nadin sarautar.
Wasu kungiyoyi da dama a arewacin Najeriya sun yi Allah’wadai da mummunan kisan gillar daya auku kan wasu matafiya da suka ratsa ta jihar Filato a ranar Asabar da ta gabata daga jihar Bauchi zuwa jihar Ondo.
Domin Kari