Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashi 80% Na Mutuwar Masu Dauke Da Cutar Covid-19, Rashin Yin Allurar Rigakafi Ne


Allurar rigakafin Covid 19
Allurar rigakafin Covid 19

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana da shaidun da ke nuni da cewa sama da kashi 80 cikin 100 na mace-macen da ake samu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 a ‘yan kwanakin nan wadanda ba’a yi musu allurar rigakafin cutar ba ne.

Da yake magana a taron wayar da kan shugabannin kungiyar daliban Najeriya ta kasa, Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya ta Kasa a matakin farko (NPHCD) Dakta Faisal Shua’ib ya ce shaidun da ke gaban hukumar sun nuna cewa yawancin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ta COVID-19 ba alluran rigakafi ne ya yi sanadiyar mutuwar su ba.

Dr. Faisal Shuaib, ya ce allurar rigakafin COVID-19 da ake yi a kasar sun tabbatar da sahihancinsu da kuma ingancinsu , ya kara da cewa an yiwa ‘yan Najeriya miliyan shida allurar rigakafi ba tare da wata illa ba.

Ya na mai cewa

“Sama da kashi 80 na wadanda suka mutu sakamakon COVID-19 su ne wadanda ba a yi musu allurar ba. Abin da bayanai suka nuna mana shi ne, sama da kashi 80 cikin 100 na mutanen da suka mutu da cutar COVID-19 a Najeriya, wadanda ba a yi musu allurar ba ne. Hakan na nufin takwas cikin 10 da suka kamu da cutar COVID-19 na iya mutuwa saboda ba a yi musu allurar rigakafi ba. Don haka muna da tabbacin cewa allurar COVID-19 na aiki da gaske’’.

A ya mai karyata dukkan zarge-zargen da ake yi na cewa duk wanda aka yi mai allurar rigakafin zai mutu .

Ya kuma yaba da ganawar da hukumar ta yi da shugabannin kungiyar dalibai ta kasa a Najeriya NANS a matsayin wata dama ta musamman ta hadin gwiwa da sauran matasan kasar wadanda sune manyan gobe inda ya bukaci al'umma su ba da hadin kai wajen karbar don kowa ya samu damar komawa rayuwarsa ta yau da kullum

A nasa bangaren shugaban kungiyar ta NANS Mista Sunday Dayo ya ce bayan tattaunawar da shugabanin kungiyar suka yi da dukkan masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya da kuma binciken da suka yi na karan kansu akan aikin ba da allurar rigakafin da hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa ta ta ke yi, su na so su tabbatarwa da al’umma ingancin allurar wanda tuni suka karba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG