Jirgin ruwan yakin Amurka ya yi harbin gargadi ga jirgin ruwan kasar Iran ta hanyar da bai dace ba.
Amurka ba zata yarda Koriya ta Arewa ta mallaki makamin Nukiliya ba, Kuma tayi kira ga Rasha da China su dauki mataki.
Kungiyar Boko Haram karkashin shugabancin Albarnawi, ta fitar da wani hotan bidiyon wasu ma’aikatan jami’ar Maiduguri guda uku da suka yi garkuwa da su.
Gwamnoni da sarakunan Arewacin Nigeria sun gudanar da taron kwanaki biyu a jihar Kaduna don yin nazari game da irin matsalolin da yankin ke fuskanta.
Yan jam’iyyar Republican a Amurka na ta kai ruwa rana don ganin sun soke tsarin inshorar kasar da ake kira Obamacare, amma har yanzu babu alamun nasara.
Wata babbar kotu dake birnin Osogbo na jihar Osun ta yankewa wani matashi hukunci kisa, bayan samunsa da laifin yiwa wata mata fashi da makamin Naira 3,420.
Hadakar kungiyar maharba masu aikin sa kai da yan kato da gora a jihar Adamawa, sunyi ikirarin cewa zasu ci gaba da taimakawa sojoji a yaki da Boko Haram muddin za’a ci gaba da tallafa musu.
Batun rage shekarun tsayawa takara da Majalisar Dattawan Najeriya ta amince na ci gaba da daukar hankan mutane, musamman masu rajin baiwa matasa dama wajen tafiyar da harkokin mulkin Najeriya.
An kaddmar da sabon jirgin ruwan yakin Amurka mai daukar jiragen sama da babu irinsa a fadin duniya.
'Yan Majalisun Tarayyar Amurka na shirin hukunta kasar Rasha da wasu takunkumi saboda katsalandan din da tayi a zaben Amurka.
Hedikwatar rundunar sojojin ruwa ta Najeriya ta girke manya-manyan jiragen yakinta har guda shida a yankin Niger-Delta.
Masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai sun bukaci al’ummar Najeriya su guji yin furuci masu harzukarwa da yada labaran ‘karya don a samu hadin kai a ‘kasa.
Mai magana da yawun fadar White House Sean Spicer ya yi murabus.
An kawo karshen sauraron shari'ar da ake yiwa Fara Ministan Pakistan kan aikata laifin cin ranci da rashawa.
Da safiyar yau Juma’a wata girgizar ‘kasa mai karfin maki 6.7 ta kashe a kalla mutane biyu ta kuma raunata sama da mutane 100 a tsibirin Kos na kasar Girka.
Mukarraban shugaban Amurka Donald Trump na neman duk wasu hanyoyin da zasu kawo cikas ga binciken da ake gudanarwa akan alakar kwamitin kamfen din Trump da kasar Rasha a zaben shugaban kasar da ya gabata.
Majalisar dokokin Kano ta jingine batun nada Hajiya Binta Fatima Yahya mace guda daya tilo dake cikin jerin mutane 44 da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ke muradin nadawa mukaman kantomomi bayan da wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar ya kare a watan jiya.
Domin Kari