An gudanar da wani taron koli na musaman da ya hada masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai daga jihohi 36 na Najeriya, mai taken ‘Furuci Masu Harzukarwa Labaran ‘Karya da Hadin Kan ‘Kasa’.
Masana a harkar yada labaran sun tattauna kan barnar da irin mugayen kalamai da wasu ke amfani da kafafen yada labarai wajen harzuwa zamantakewar al’ummar Najeriya.
A cewar Ministan yada labaran Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, dole ne ‘yan Najeriya su gujewa furuci masu tsauri dake harzuka al’umma da haddasa rabuwar kawuna a kasar.
Manufar taron shine tattaunawa don warware matsalar yada labarai a Najeriya,
Domin karin bayani ga rahotan Zainab Babaji.
Facebook Forum