Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kaddamar Da Wani Sabon Jirgin Yaki Da Babu Irinsa a Duniya


Jirgi USS Gerald R. Ford
Jirgi USS Gerald R. Ford

An kaddmar da sabon jirgin ruwan yakin Amurka mai daukar jiragen sama da babu irinsa a fadin duniya.

Shugaba Donald Trump ya jagoranci kaddamar da jirgin ruwan daukar jiragen sama na yaki mai suna USS Gerald R. Ford, wanda aka kera da fasahar zamani, akan dala kusan biliyan 13, wanda a cewarsa, jirgin ya aika da sakon gargadi mai nauyin ton "100,000 ga duniya," kuma zai sa abokan gaban Amurka su kadu sosai saboda tsoro."

Bayan jinkiri na tsawon shekaru uku da kuma karin biliyoyin da aka kashe, Trump ya danka kammalallen jirgin na daukar jiragen yaki mai aiki da karfin nukiliya, irinsa na farko a duniya, ga rundunar sojojin ruwan Amurka, a wata tasharsu ta Norfolk a jahar Virginia da ke kudu maso gabashin kasar.

Shugaban ya ce jirgin yakin na aikin tauna tsakuwa, ta yadda ba ma sai an yi yaki ba, to amma sai ya kara da cewa, muddun kuma yaki ya auku, abin da zai sake faruwa shi ne, "za mu yi nasara, mu kuma yin nasara"

Bayan da ya caccaki gwamnatin da ta gabata, saboda abin da ya kira "Rashin kyakkyawan shiri irin na soji," sai Trump ya yi kira ga Majalisar Tarayya da ta yi aikinta ta wajen samar da kuddaden gudanarwa ga bangaren soji.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG