Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da wasu batutuwa guda 30 domin su zama wani bangare na kudin tsarin mulkin Najeriya, a yunkurin yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima.
Batutuwan guda 30 sun hada da rushe hukumomin zabe na jihohi da daidaita wa’adin shugabannin kananan hukumomin kasar guda 774 zuwa tsawon shekaru uku da samar da gurbin tsayawa takarar gashin kai a kundin tsarin mulki kasa da kuma baiwa kananan hukumomi kudade kai tsaye daga Tarayya, da sauya gurbi daga hurumin yin wasu dokoki da nade-naden mukaman gwamnati daga bangaren zartarwa zuwa Majalisar Dokoki ta kasa.
Yanzu haka dai an rage mafi karancin shekarun masu tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya daga 40 zuwa 35, sai kuma na gwamna daga 32 zuwa 30, sai Majalisar Wakilai daga 30 zuwa 25.
Matasan Najeriya sunyi maraba ga wannan sabon tsari, Kwamrad Kabiru Sa’idu Dakata, na ganin wannan yunkuri ne da zai taimakawa harkar shugabanci a Najeriya, ganin yadda dattawan da suka dade suna mulki suka kasa shawo kan matsalolin kasar.
Shi kuma Kwamrad Abdullahi Kwalwa, mai sharshi kan lamuran siyasa na ganin an makara wajen bijiro da wannan tsari.
Batun kashe kudade a harkokin siyasar Najeriya na daga cikin al’amuran da ake hasashen zai kawo cikas ga damar da matasan suka samu. Bayan samun amincewar Majalisar Dokoki ta kasa tilas ne duk wani batu da zai samu gurbi a kundin tsarin mulkin Najeriya, sai ya samu goyon bayan kashi biyu bisa uku na yawan ‘yan Majalisun Dokokin jihohin kasar, kafin daga bisani ya zama doka.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum