Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Fitar Da Bidiyon Ma’aikatan Jami’ar Maiduguri Da Ta Yi Garkuwa Da Su


Kungiyar Boko Haram karkashin shugabancin Albarnawi, ta fitar da wani hotan bidiyon wasu ma’aikatan jami’ar Maiduguri guda uku da suka yi garkuwa da su.

A ranar 25 ga watan Yuli ne ‘yan kungiyar Boko Haram bangaren al-Barnawi suka hallaka mutane da dama ciki har da masu hakan man fetur da malaman jami’ar Maiduguri da kuma sojojin Najeriya, a wani harin kwantan bauna da tayi musu, inda sukayi garkuwa da wasu ma’aikatan.

Sai gashi kungiyar ta saki sabon hotan bidiyo dake nuna ma’aikatan jami’ar da aka yi garkuwa da su suna rokon gwamnatin Najeriya da ta sa hannun domin kubutar da su.

Anyi ta samun bayanai masu karo da juna tsakanin jami’ar Maiduguri da kuma rundunar sojan Najeriya, da tayi ikirarin cewa ta samu kubutar da dukkannin ma’aikatan dake tono ma’adanin man fetur dake yankin da aka yiwa kwantan bauna tsakanin kananan hukumomin Magumeri da Gubio

Kungiyar malaman jami’ar Maiduguri ta fito tace lamarin ya shafi ma’aikatanta guda tara, wanda kuma tuni an kawo gawar mutane biyar saura hudun kuwa ba a san inda suke ba,

Hotan bidiyon da kungiyar Boko Haram din ta fitar ya nuna wasu mutane uku da suka bayyana kansu ‘daya bayan ‘daya suna tabbatar da cewa su ma’aikatan jami’ar Maiduguri ne, kuma yanzu haka suna hannu ‘yan kungiyar Boko Haram.

Ma’aikatan dai sun yi kira ga gwamnatoci da suka hada da na tarayya da jiha, da jami’ar Maiduguri da kuma kamfanin matatar Man Fetur da su biyawa maharani bukatunsu don a sako su da ransu.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG