Yayin da wa’adin sintirin Operation Tsare Teku ke zuwa karshe, rundunar sojan ruwa ta ‘kara wa’adin ci gaba da gudanar da sintirin.
A cewar kakakin hedikwatar sojojin ruwan Najeriya, Captain Suleman Dahun, rundunar ta ‘dauki matakin ne domin kawo karshen ‘yan fashin teku, inda yace a shekarar da ta gabata sun kai hare-hare har 55 inda suka sami nasara har sau 36.
Masana harkokin tsaro a Najeriya, na ganin matakin yazo a dai-dai lokacin da ya dace.
Masanin tsaro Ahmed Tijjani Baba Gamawa, na ganin wannan na kama da wanda ‘yan magana kan kira na ‘ayita ta kare’ ganin yadda aka girke manya-manyan jiragen yaki har guda shida baya ga masu saukar ungulu daga sama.
Abin jira a gani shine irin yadda wannan karin lokaci zai shafi sha’anin tsaro a yankin Niger-Delta.
Domin karin bayani ga cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum