Kotu ta yankewa Kayode Adedeji hukuncin rataya bayan da ta same shi da laifin aikata fashi da makami. Adedeji dai ya yiwa Omowumi Adebayo fashi da wuka cikin dare inda ya karbe mata kudi har Naira 3,420.
Duk da yake masana shari’a na ganin hukuncin da kotun ta yanke ba wani abin mamaki bane, duba da tsarin dokar Najeriya kan fashi da makami. Amma wasu ‘yan Najeriya na ganin hukuncin yayi tsauri dayawa idan akayi la’akari da yawan kudin da aka sata.
A cewar Barista Yusuf Musa Funtua, wannan hukunci bai zo da mamaki ba, duba da yadda tsarin dokokin da suka bayyana hukuncin fashi da makami a Najeriya, wanda hukucin fashi da makami ba yana la’akari da yawan kudi ko abin da akayi fashin akai ba.
Ganin cewa akan samu mutane masu yawa da laifin sace Biliyoyin Naira a Najeriya, amma ba a yanke musu hukunci mai tsanani irin wannan ba. da yake karin haske kan wannan batu, Barista Yusuf, ya ce sata daban take, shima fashi da makami daban yake.
Kashin dokokin da ya tanadi hukunce-hukunce akan laifuka ya tanadi cewa duk wani da yayi sata ta hanyar yin amfani da barazana ko karfi akan wanda zai yiwa satar ya aikata fashi da makami, hukuncin laifin kuma ya hada da zaman gidan Yari har shekaru 21, haka kuma dokar ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya aikata da makami.
Da suke bayyana ra’yoyinsu wasu ‘yan Najeriya na ganin hukuncin yayi tsauri sosai idan akayi la’akari da kankantar kudin da Kayode Adedeji ya sata.
Domin karin bayani ga rahotan Hassan Umaru Tambuwal.
Facebook Forum