Daruruwan masu zanga-zanga akan rashin wutar lantarki a jihar Neja sun rufe babbar hanyar motar da ta hada Minna zuwa sokoto da Birnin Kebbi da kuma Kontagora.
Jam’iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da gudanar da zabukan cikin gida domin fitar da ‘yan takarar mukamai daban-daban a babban zaben kasar da aka shirya gudanarwa cikin watan Fabarairun badi.
Ciki da Gaskiya Wuka Ba Ta Hudashi
Hukumomin tsaro a jihar Filato sun bukaci al’umma dake ciki da wajen jihar da su gargadi matasa dake neman tayar da zaune tsaye a jihar su rungumi zaman lafiya.
Shugaban Kamaru Paul Biya ya ce ya yi nasarar fatattakar 'yan Boko Haram daga cikin kasar, don haka da matukar bukatar sake zabensa a zaben Shugaban kasar na ranar 7 ga watan Oktoba, saboda ya sake farfado da abubuwan da su ka durkushe.
Fadar Shugaban Amurka ta White House, jiya Lahadi, ta ce sam ba ta jujjuya binciken da hukumar FBI take yi ma mutumin da aka gabatar da sunansa don zama Alkalin Kotun Kolin Amurka, Brett Kavanaugh.
A jihar Adamawa cikin tsauraran matakan tsaro aka gudanar da zaben fidda gwanin na babbar jam’iyar adawa ta PDP da kuma jam’iyar APC mai mulki a jihar.
Jam’iyyar APC mai mulki ta dage zaben fidda gwani na ‘yan takarar gwamna a jihohi shida, da su ka shafi kusan dukkan yankunan Najeriya.
Kasar China na yin amfani da wasu dabaru wajen kai wa Amurka hare-hare ta yanar gizo, da nufin tattaro bayanan wasu kwamitocin gudanarwa na jam'iyyun siyasa.
A fadin duniya mutane bakwai cikin goma na mutuwa ne sanadiyar cututtukan da suka hada da hawan jini da ciwon daji da ciwon siga da mummunan ciwon huhu, a cewar wani bincike da aka kafe a fitatciyar mujallar The Lancet cikin wannan watan.
Ranar Litinin uwar gidan shugaban Amurka Melania Trump za ta fara ziyararta ta farko zuwa kasashen waje tun da mijinta ya hau kan mulki, yayin da za ta ziyarci kasashen Afirka hudu domin yada shirinta na inganta rayuwar yara mai suna “Be Best” wato kasance na gari.
Ciki da gaskiya wuka ba ta hudashi
Fransa da kasar Italiya suna sabanin ra'ayi game da yadda za'a kawo a sauyi a Libya, bayan kawar da gwamnatin marigayi Moammar Gaddafi.
Wata mujallar Amurka The New Yorker ta bada rahoton cewa wata wata mace daban tana zargin Alkali Brett Kavanaugh, wanda shugaban Amurka ya zaba domin zama alkali a kotun koli na Amurka.
Shugaban 'yan tawaye a Sudan ta kudu Rik Machar, yayi watsi da gayyatar da shugaban kasar Salva Kiir yayi masa a jiya Asabar, ya kai ziyara Juba babban birnin kasar.
Gabanin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, masu neman takara a jam’iyyar na ci gaba da mara baya ko fadar abin da su ke son a yi don gudun korafi ko ma tafiya kotu a sakamakon zaben.
Yawan mutanen da suka mutu ya ‘karu zuwa 167 an kuma ceto mutum daya da rai jiya Asabar, bayan da jirgin ruwa ya nutse a tafkin Lake Victoria na kasar Tanzaniya ranar Alhamis.
Jiya Asabar ne wasu ‘yan bindiga sun bude wuta a wajen wani faretin sojoji a Kudu maso yammacin Iran, inda suka kashe akalla mutum 25 da raunata wasu 60, a cewar kafar yada labarai ta gwamnati.
Dangantaka tsakanin Amurka da China na 'kara tabarbarewa bayan da Amurkar ta 'kara haraji kan kayayyakin da China ke shigarwa Amurka, sai kuma takunkumin da ta sakawa China biyo bayan sayen makamai da ta yi daga kasar Rasha.
Shirin na ci gaba da bin diddigin zargin rashawa da wani Bako Waziri yayi wa shugaban ma'aikatan Shugaban Najeriya, Abba Kyari na cewa ya karbi kudi domin wata kwangilar siyo motoci. Ciki da gaskiya, wuka ba ta huda shi!
Domin Kari