Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Zargin Kavanaugh Da Yunkurin Wata Lalata


Wata mujallar Amurka The New Yorker ta bada rahoton cewa wata wata mace daban tana zargin Alkali Brett Kavanaugh, wanda shugaban Amurka ya zaba domin zama alkali a kotun koli na Amurka.

Mujallar ta ruwaito jiya Lahadi cewa, sanatoci biyu suna binciken zargin da wata mace tayi kan alkalin cewa, ya tsiraita kansa a gabanta, lamari da ya tilasta mata taba gabansa lokacin da take ture shi. Matar Deborah Ramirez, 'yar shekaru 53 tayi zargin cewa lamarin ya auku ne a shekarar karatun 1983-84, a jami'ar Yale a lokacin wata liyafa.

Sai dai mujallar tace zuwa yanzu bata sami wani shaida da zai gaskanta wannan zargi ba.Koda shike wadanda suka yi karatu da alkali Kavanaugh sun ce wannan ba halinsa ba bane, wadanda suka san Deborah kuma sun mata kyakkawar shaida, har suka ce sun tuna ganin mai shari'a Kavanaugh zamanin yana dalibi ko da yaushe cikin maye.

Fadar White House ta fidda sanarwa daga alkali Kavanaugh tana cewa mai shari'a Kavanaugh ya musanta wannan zargi kuma ta ci gaba da cewa wannan ba wani abu bane a fili "illa bata suna."

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG